Tirkashi: Sojoji sun kai mamaya hedkwatar yan sanda dake Osun

Tirkashi: Sojoji sun kai mamaya hedkwatar yan sanda dake Osun

Wasu sojoji dauke da makamai, a ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba, sun kai mamaya hedkwatar rundunar yan sandan jihar Osun a Osogbo sannan suka fasa kofar inda suka haifar da tashin hankali a yankin.

A cewar wasu masu kasuwanci a kusa da hedkwatar yan sandan, tuni sojoji uku suka shiga harabar kafin aka tsayar da sauran a bakin kofar shiga.

Wata yar kasuwa, wacce ta bayyana kanta a matsayin Nkechi, ta yi ikirarin cewa mutane da dama dake kasuwanci a yankin sun yi gaggawan rufe wurarensu domin taoron kada abun ya cika da su.

Ta fada ma manema labarai cewa kimanin sojoji 25 aka gano a kofar shiga hedkwatar rundunar inda suke zazzafan musayar yawu da yan sandan yankin da misalin karfe 1:00 na rana.

“Daga bisani sai wani babban dansa mai suna Edward Ebuka, ya sanya baki sannan sojojin suka bari yankin,” inji Nkechi.

Wata babbar majiya wacce ta nemi sakaya sunanta ta fada ma jaridar Punch cewa, yan sanda sun kama sojoji uku da suka shiga harabar, yayinda sauran suka wuce.

Yace dalilin zuwan sojojin yankin baya rasa nasaba da kama wani soja a ranar Asabar akan wani laifi da ba a sani ba.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: Rigima ya kaure tsakanin majalisar wakilai da ministar Buhari a wajen kare kasafin kudi

Da aka tuntube shi don jin ta bakinta, jami’ar hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, Folasade Odoro, bata tabbatar ba kuma bata karyata lamarin ba.

“Za a yi jawabi ga manema labarai kan abunda ya faru bada jimawa ba,” inji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel