Kaico! Yarinya mai shekaru 13 ta kashe yayarta tare da farke cikinta don cire jariri

Kaico! Yarinya mai shekaru 13 ta kashe yayarta tare da farke cikinta don cire jariri

‘Yan sandan kasar Brazil sun cafke wata yarinyar mai shekaru 13 akan laifin kashe yayarta bayan da ta fasa cikin yayar don cire jariri.

Kamar yadda rahoton ya nuna, karamar yarinyar ta yi kisan ne bisa ga umarnin wata mata mai shekaru 35. Matar ta so karbar jinjirin ne don rainonsa a matsayin danta, kamar yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito.

Fabiana Santana mai shekaru 23 tana da cikin wata 8 lokacin da yarinyar ta kai mata farmakin.

Ruwa ya tafi da dan Santana mai shekaru 7 yayin da yayi yunkurin tseratar da mahaifiyarsa a Porto Velho, Brazil.

An daketa da karfe a kai inda fuskarta ta lalace bayan nan aka soketa da wuka.

DUBA WANNAN: Matar da ta auri maza uku ta zubasu a gida daya

‘Yan sandan sun bayyana cewa, yarinyar ta aiwatar da aika-aikar ne da taimakon wani dan shekaru 15 karkashin umarnin Catia Rabelo.

An cafke matar da ta sasu mai suna Catia Rabelo a ranar Laraba bayan da ta tsere amma ta amsa laifinta na tsara komai da saka kananan yaran.

An gano cewa, Rabelo ta so amfani da jaririn ne don damfarar saurayinta da ta cewa tana da cikinsa.

Abin dadin shine, ’yan sanda sun samu jainjirin da ransa a wajen yaron mai shekaru 15 da ya taya aikata laifin. Mahaifiyarsa da bata nan yayin da suka aikata laifin ta tsere ta bar gidan.

A halin yanzu jinjirin na asibitin Porto Base Old don samun kular masana kiwon lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel