Tabbas ana tafka badakala a daukar aikin gwamnati - Shugaban ma'aikatan FG

Tabbas ana tafka badakala a daukar aikin gwamnati - Shugaban ma'aikatan FG

- Mukaddashin shugabar ma'aikatan tarayya, Mrs Yemi Esan, ta zargi rashin gaskiya ta wajen daukar aiki

- Ta sanar da hakan ne a yayin da take kare kasafin kudin ma'aikatarta na shekarar 2020

- Ta bayyana yadda takardun daukar aiki da karin girma na bogi ke kai-kawo don neman sa hannunta

Mukaddashin shugabar ma'aikatan tarayya, Mrs Yemi Esan, ta zargi cewa akwai rashin gaskiya ta wajen daukar aiki a kusan duk ma'aikatun tarayya, bangarori da cibiyoyin gwamnati.

Ta tabbatar da hakan ne a jiya yayin da take amsa tambayoyin kwamitin majalisar wakilai a lokacin da take kare kasafin kudin ma'aikatar da take shugabanta.

DUBA WANNAN: Gwamnoni sun cimma sabuwar matsaya a kan biyan sabon karin albashi

Kamar yadda tace, mutane da yawa wadanda suka hada da ma'aikatan da ba na gwamnati ba un fada cikin mummunar dabi'ar. Tace, masu mummunar dabi'ar kan rubuta takardun daukar aiki da karin girma na bogi wadanda suke kaiwa ofishinta don ta sa hannu.

Tace, ganin takardun daukar aiyuka na bogi ne yasa aka assasa tsarin biyan albashi na IPPS. Tace, akwai ma'aikata 77,651 na gwamnatin tarayya da ke karkashin ma'aikatu, bangarori da cibiyoyi a halin yanzu.

Shugabar ma'aikatan ta ce, kasafin kudin shekarar 2020 ya kai naira biliyan 48 don aiyukan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel