Ba mu ce Buhari ya canja wa Najeriya suna ba - Ohanaeze Ndigbo

Ba mu ce Buhari ya canja wa Najeriya suna ba - Ohanaeze Ndigbo

Kungiyar kabilar Ibo, Ohanaeze Ndigbo ta nesanta kanta daga wata sanarwa da aka alakanta da kungiyar na neman a canja wa Najeriya suna.

Mataimakin sakataren yada labarai na kasa na kungiyar, Chuks Igegbu, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ya ce, ya kamata a canja wa kasar suna don sunan na da alaka da "rashin cigaba, rashawa da duhu".

Ibegbu ya ce "Budurwar Lord Lugard ce ta sanya ma kasarmu suna Najeriya, wanda daga bisani ta zama matarsa, kuma cikin shaukin soyayya ne ta sanya ma kasarmu wannan suna."

Ya kara da cewa, "Kasashe duniya a Afirka, Asia har ma da Turai cun canja sunayensu bayan samun 'yanci amma saboda sakarci mun cigaba da amfani da tsohon sunan duk da matsalolin da ke tattare da shi."

DUBA WANNAN: Wani mutum ya 'mutu' ya dawo bayan shekara 30 a Kano

"Ina kallubalantar 'yan Najeriya su kir taron cikin gaggawa inda za a zabi sabon suna irin ta mu ta kasa."

Ibegbu ya ce, "Idan ba mu canja sunan mu ba, matsalolin mu ba za su taba karewa ba domin suna linzami ne."

Sai dai shugaban Ohanaeze Ndigo na kasa, Cif John Nwodo ya ce kungiyar ba ta bashi damar fitar da wannan sanarwar ba saboda haka ba wannan zancen ra'ayinsa ne kawai ba matsayar kungiyar ba.

A hirar da ya yi da The Punch a wayar tarho, Nwodo ya ce za a binciki Ibegbu kuma a halin yanzu an haramta masa fitar da sanarwa a madadin kungiyar.

Tsohon ministan Al'addun ya ce, "Ibegbu ya fadi ra'ayinsa ne kawai. Ohanaeze Ndigbo ba ta bashi izinin fitar da wannan sanarwar ba don ba shine matsayar ta ba.

"Sanarwar da ya fitar ta sabawa hankali hakan yasa yanzu aka haramta masu fitar da sanarwa a madadin Ohanaeze Ndigbo ta tare ya nemi izini ba. An kuma aike masa wasikar neman ba'asi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel