Wata sabuwa: Fulani ne za su shiga halin ni 'yasu idan Najeriya ta rabu gida biyu - Tsohon gwamnan Anambra

Wata sabuwa: Fulani ne za su shiga halin ni 'yasu idan Najeriya ta rabu gida biyu - Tsohon gwamnan Anambra

- Tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana cewa idan har Najeriya ta rabe gida biyu kabilar Fulani ne za su fi shan bakar wahala a kasar nan

- Ya ce al'ummar Igbo suna ta faman korafi akan yanayin mulkin shugaba Buhari akan irin wariyar da yake nuna musu

- Ya kara da cewa Fulani sune suke da dukkanin madafun iko na kawo gyare-gyare a kasar nan, don haka ya kamata suyi amfani da damar su

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Dr. Chukwuemeka Ezeife, ya bayyana cewa Fulani ne za su sha bakar wahala idan har aka raba Najeriya gida biyu.

Da yake hira da wakilan jaridar The Sun, tsohon gwamnan jihar Anambran ya ce al'ummar Igbo suna ta faman korafi akan abubuwa da dama da ake yi musu, ya kara da cewa gwamnatin shugaba Buhari tana nema ta kai su zuwa ga bango, ta hanyar nuna musu wariya.

A cewar shi, "Babu wanda yake so ya zama bawa a Najeriya, ko suna so ko basu so kaine shugaban su, kuma kana da iko fiye da su, amma mai yasa muke fuskantar irin wannan matsalar a wannan lokacin? Babu wani cigaba da ake samu a kasar nan."

KU KARANTA: Tun da Sallah aka sace yarona a Kano, sai yanzu aka samo shi a Anambra - Muhammad Ali

"Duk mutumin da ya hau doki shi dokin zai jiwa ciwo idan dokin ya fadi, saboda haka su sauko daga kan dokin koda za a samu zaman lafiya koda dokin ya fadi babu wanda zai ji ciwo."

"Idan ace ni Hausa ne ko Fulani, ko dan bari na cire Hausawa a ciki, saboda su za su nemi hanyar da zasu kawar da matsalar idan ta faru, amma Fulani sune za su sha bakar wahala idan har Najeriya ta rabu gida biyu, kuma sune suke da mukaman da za su kawo karshen wannan matsalar ta hanyar kawo ayyuka na cigaba a kasar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel