Tun da Sallah aka sace yarona a Kano, sai yanzu aka samo shi a Anambra - Muhammad Ali

Tun da Sallah aka sace yarona a Kano, sai yanzu aka samo shi a Anambra - Muhammad Ali

- Wani mutumi ya ya bayyana yadda aka samo dan shi a jihar Anambra tun bayan batan da yayi a jihar Kano

- Daya daga cikin mahaifan yaran nan da aka ceto a jihar Anambra ya bayyana yadda aka yi garkuwa da dan shi

- Mutumin ya bayyana cewa shi gaba daya sai da ya cire rai da zai kara ganin dan shi kwatsam ake fada masa cewa ya zo an samu dan shi

"A lokacin da 'yan sanda suka bayyana mini cewa za su je jihar Anambra domin binciken wasu yara da suka bata, ban taba tunanin cewa wannnan bincike na su zai yi sanadiyyar dawowar dana gida," in ji Muhammad Ali.

Dan gidan Muhammad Ali mai shekaru biyar a duniya yana daya daga cikin yaran da 'yan sandan jihar Kano suka kubutar daga jihar Anambra.

"Bayan 'yan kwanaki suka kirani a waya cewar sun dawo, mu zo mu duba ko akwai dan mu a ciki. Cikin sauri na garzaya zuwa ofishin su kawai sai ganin dana nayi Usman, tsananin dadi yasa na dinga zubar da hawaye. Nayi godiya ga Allah da kuma Mr. Babagana (Wanda ya jagoranci rundunar binciken yaran)."

Mutumin dai yana zaune a Sauna Kawaji ne, cikin karamar hukumar Nasarawa, ya sanar da jaridar Premium Times yadda aka sace dan shi a lokacin bikin sallah da aka yi wannan shekarar.

KU KARANTA: Saudiyya za ta koma Aljannar duniya: Za a shuka bishiyoyi kala-kala har guda miliyan 5 a kasar Saudiyya

"Kwana biyu da Sallah Usman ya fita ziyara gidan kannaina, a nan ne suka samu suka ja hankalin shi suka gudu da shi. Munyi ta faman neman shi amma bamu ganshi baba. Sai muka kai kara wajen jami'an 'yan sanda sannan muka bar wa Allah ikon sa."

"Ina fata gwamnati za ta yi iya bakin kokarinta wajen ceto sauran yaran da suka bata sannan ta yanke hukunci kan wadanda suke da hannu a lamarin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel