Wata sabuwa: Inyamurai sun nemi Buhari ya canza sunan Najeriya

Wata sabuwa: Inyamurai sun nemi Buhari ya canza sunan Najeriya

A wani mataki mai kama da wasan yara, kungiyar kabilar Inyamuran Najeriya,Ohanaeze Ndigbo ta yi kira da a canza ma Najeriya suna zuwa wani sabon suna mai ma’ana, idan har ana son samun cigaba a kasar.

Jaridar The Nation ta ruwaito kungiyar ta bayyana haka ne a ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba ta bakin mataimakin mai magana da yawunta, Chuks Ibegbu inda yace sunan Najeriya na nufin matsala, duhu da kuma cin hanci da rashawa.

KU KARANTA: Dan bindiga mai shekaru 84 ya bindige Musulmai 2 a Masallacin kasar Faransa

A jawabinsa, Chuks yace: “Budurwar Lord Lugard ce ta sanya ma kasarmu suna Najeriya, wanda daga bisa ta zama matarsa, don haka kowa ya san cewa a cikin shaukin soyayya ta sanya ma kasarmu wannan suna.

“Yayin da sauran kasashen Afirka suka sauya sunayensu bayan samun yanci, amma a wawancimu mun cigaba da amfani da sunan Najeriya, idan har ba a canza sunan nan ba matsalolinmu ba zasu taba karewa ba, saboda akwai sirri a cikinsu, suna linzami ne.

“Duk da yake muma bamu gano wanda ya sanya mana sunan Igbo ba, amma a duk ranar da muka fahimci akwai wata matsala tattare da asalin sunan, tabbas zamu canza shi, don haka ba Ibo muke ba, sunanmu Igbo ko Ndigbo.” Inji shi.

Bugu da kari, Chuks ya yi kira ga dukkanin kabilun Najeriya dasu shirya babban taron jin ra’ayi domin musayar ra’ayi game da sunan daya dace a sanya ma Najeriya, a cewarsa ta haka ne kawai Najeriya za ta da dace da kyakkyawan suna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel