Dan bindiga mai shekaru 84 ya bindige Musulmai 2 a Masallacin kasar Faransa

Dan bindiga mai shekaru 84 ya bindige Musulmai 2 a Masallacin kasar Faransa

Wasu Musulmai biyu masallata sun samu munana rauni sakamakon wani harin ta’addanci da wani dan bindiga ya kaddamar a wani Masallaci dake garin Bayonne na yankin kudu maso yammacin kasar Faransa.

Rahoton gidan talabijin na Channels ta bayyana cewa jami’an Yansanda sun samu nasarar kama wannan matsiyacin dan bindiga da bincike ya nuna shekarunsa sun kai 84, inda aka kamashi a kusa da gidansa bauan ya kai harin ya kom gida.

KU KARANTA: Ragas! Jami’in Dansandan Najeriya ya bindige matarsa, ya halaka kansa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dan bindigan ya yi amfani da wasu ababen fashewa daya tayar a daidai kofar masallacin, wannan ne yasa masallata guda biyu wanda dukkaninsu sun kai shekaru saba’in saba’in, suka tinkareshi.

Shi kuma ganin sun tunkaro shi ne yasa dan ta’addan ya bude musu wuta, a sanadiyyar haka suka samu munana rauni, wanda a yanzu haka suna samun kulawa a wata babbar asibitin kasar Faransa.

Tun daga ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba da wannan lamari ya auku, Yansanda sun hana shige da fice a yankin Masallacin domin gudanar da cikakkiyar bincike.

Wannan hari dai ya faru ne jim kadan bayan shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya yi kira ga al’ummar Musulman Faransa dasu taimaka wajen yaki da yan ta’adda biyo bayan hari da wani musulmi ya kai a wajen aikinsa, inda ya kashe abokan aikinsa guda hudu da wuka.

Idan za’a tuna hare haren yan bindiga a Masallatan kasar Faransa ba sabon abu bane, inda ko a watan Yunin data gabata sai da wani dan bindiga ya harbi limamin Masallaci a birnin Brest.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel