Babban magana: Rigima ya kaure tsakanin majalisar wakilai da ministar Buhari a wajen kare kasafin kudi

Babban magana: Rigima ya kaure tsakanin majalisar wakilai da ministar Buhari a wajen kare kasafin kudi

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Ikwunano/Umuahia arewa/kudu na jihar Abia, Mista Ifeanyi Onuigbo, ya kara da ministar harkokin mata, Pauline Tallen a Abuja a ranar Litinin, 29 ga watan Oktoba.

Rikicin ya kaure ne lokacin da ministar ta gurfana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin mata domin kare kasafin kudin 2020 da ma’aikatarta ta gabatar.

A lokacin da manema labarai suka shiga zauren, tuni Onuigbo ya fara kumfar baki, inda ya bukaci shugabar kwamitin, Adewunki Onaniga da ta bari ya yi magana, wanda ta yi kokarin tausar shi.

Onuigbo ya ce: “Mun lura cewa ba ma bisa tafarkin da ya kamata kuma muna neman hanyoyin tabbatar da samun cigaba domin ma’aikatar harkokin mata da cigaban jama’a. Wannan shine matsayinmu. Bai kai ga ambatan suna ba, yin haka, daga wani da ya shigo a matsayin minista domin mu daura shi ko ita bisa hanya. Ba zan lamunci haka ba gaskiya."

Shugabar ta tambayi ko Tallen ta ambaci kowani suna.

Onuigbo ya ce: “ta yi nuni, cewa wadannan mambobin guda biyu. Saboda haka, wannan ba karbabbe bane. Madam, ya zama dole na fadi wannan, koda kuwa hakan na nufin ba zan dawo wannan kwamitin ba. Ina magana ne akan abu mai matukar muhimmanci. Ba zai yiwu ki zo nan ki zauna sannan kiyi furuci irin haka ba. Ba zan lamunci haka ba. Ni babban mamba ne."

Shugabar kwamitin ta hana Tallen, wacce ta yi yunkurin mayarwa Onuigbo martani.

Onanuga ta ce: “Mai girma Onuigbo, dan Allah, a madadin mata da ma’aikatar da kuma wannan kwamitin, Ina mai baka hakuri. A matsayina na shugabar wannan kwamitin, Ina mai baka hakuri. Bana tunanin ita (Tallen) ta yi nufin abun a yadda ya zo.”

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda aka yi jana’izar matar Tafawa Balewa a Bauchi

Shugabar ta nemi a dage zaman kuma aka amince.

Tallen, bayan taron ta tunkari yan majalisa, ciki harda Onuigbo, a kan abunda ya yi kama da yunkurin yin sulhu.

Tallen ya fada ma manema labarai cewa “An daidaita komai. Ya kamata ku san yadda yan siyasa ke magana wasu lokutan. Babu wani sabon abu a ciki kuma an sulhunta komai."

Ministar ta ce an bukaci ta gabatar da cikakken bayani akan kokarin kasafin kudin ma’aikatar a shekarun baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel