Lawan: Dole Gwamnatin Najeriya ta dakatar da cin bashin kudi

Lawan: Dole Gwamnatin Najeriya ta dakatar da cin bashin kudi

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, yace dole Najeriya ta dakatar da cin bashin da ta ke yi. Sanatan yace kasar ta na cin bashi ne saboda hukumomin da ke da alhali sun yi kasa a gwiwa.

Sanata Ahmad Lawan ya zargi hukumomin da ke tatsowa gwamnati kudin shiga da cewa ba su yin aikin da ya kamata. Shugaban majalisar ya bayyana wannan ne wajen yaye wasu ‘Dalibai.

Kamar yadda Hadimin shugaban majalisar dattawan ya bayyana, Lawan ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi jawabi wajen yaye ‘Daliban jami’ar Benin da kuma wata babbar cibiyar kasar.

A jawabin da Ezrel Tabiowo ya fitar da yawun shugaban Sanatocin, ya ce: “Yau Najeriya ta na fama da karancin arziki. Za mu iya amincewa da kasafin kudi a lokacin da ba a taba yi ba a tarihi.”

KU KARANTA: Ana rikici tsakanin Gwamnatin Buhari da Jami’o’i a kan tsarin IPPIS

“Sai dai idan aka zo maganar dabbaka kasafin, sai a fara maganar nawa Najeriya ta samu a matsayin kudin shiga. Mafi yawan wadannan hukumomi ba su ba gwamnati abin da su ka tatso.”

“Sun sa dole gwamnatin tarayya ta buge da cin bashi. Lokaci ya yi da majalisa za ta rika tuntubar hukumomin da ke da alhakin tatso kudi domin su ji kalubalen da su ke fama da su.” Inji Lawan.

Sanatan bai tsaya nan ba, ya cigaba da cewa: “Burinmu shi ne mu karkare aikin kasafin kudin nan kafin Kirismeti. Gobe (29 ga Wata) ne ranar karshe da ma’aikatu za su kare kasafinsu a majalisa.”

Majalisa ta na so ace an kammala duk wani aikin kasafiin kudi kafin karshen Disamba inda za a tafi hutun kirismeti. Wannan zai bada damar a fara aiki da kasafin a farkon sabuwar shekara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel