Ragas! Jami’in Dansandan Najeriya ya bindige matarsa, ya halaka kansa

Ragas! Jami’in Dansandan Najeriya ya bindige matarsa, ya halaka kansa

Wani jami’in rundunar Yansandan Najeriya, mai mukamin Sufeta, ya dirka ma matarsa harsashi sakamakon wata takaddama data kaure a tsakaninsu, sa’annan ya juya bindigar a kansa ya dannan kunamar.

Rahoton jaridar The Nation ta ruwaito cewa jami’in Dansandan da aka bayyana sunansa a matsayin Edward yana cikin halin maye ne a lokacin da ya aikata wannan danyen aiki bayan ya dira gidansu dake barikin gandurobobi.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Fursunoni 200 sun tsere daga Kurkukun Kogi sakamakon ambaliyan ruwa

Rahotanni sun bayyana cewa ita ma atar Edward jami’ar ganduroba ce, toh amma zama ya kasa yin dadi a tsakaninsu sakamakon zarge zarge da ake yawan samu da rashin amintar juna, saboda haka sun dade suna takun saka da kuma rikici a bainar jama’a.

Sai dai a wannan karo, da daddaren Asabar, 26 ga watan Oktoba, sai da Edward ya sha giyansa ya yi tatil sa’annan ya shiga gidan nasu, koda yake matarsa ta kashe auren da kanta, amma sun cigaba da zama a gida daya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito makwabtansu sun bayyana cewa sun jiyo muryarsu duka a sama suna fada ma juna bakaken maganganu yayin da suke tsaka da rikicin, daga nan ashe Edward ya dauki bindigarsa, sai dai suka ji karar bindiga, ya harbi matar a kai, ganin haka yasa shima ya bindige kansa.

Ba tare da wata wata ba makwabtan suka garzayo gidansu, inda suka debesu ranga ranga zuwa asibiti, amma duk da kokarin da liktioci suka yi don ceto rayukansu hakan bai yiwu ba, inda matar ta mutu a ranar Lahadi, daga bisani Edward ma ya mutu.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Legas, DSP Bala Elkana ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kara da cewa tuni sun kaddamar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel