Yan Najeriya miliyan 90 ne ke cikin halin matsanancin talauci – Ministan Buhari

Yan Najeriya miliyan 90 ne ke cikin halin matsanancin talauci – Ministan Buhari

Akalla mutanen Najeriya su miliyan 90 ne suke cikin halin matsanancin talauci inji ministar ma'aikatar ayyukan agaji da kula da ibtila’I, Hajiya Sadiya Umar Faruk, inda tace don haka gwamnati ta yanke shawarar fitar dasu daga cikin wannan kangi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Sadiya ta bayyana haka ne yayin da take gabatar da kasafin kudin ma’aikatarta na shekarar 2020 a ranar Litinin wanda ya kai naira biliyan 44.21 domin neman sahhalewar majalisar dokokin kasar nan.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Fursunoni 200 sun tsere daga Kurkukun Kogi sakamakon ambaliyan ruwa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sadiya ta gurfana gaban kwamitin majalisar wakilai dake kula da yan gudun hijira ne a karkashin jagorancin Mohamemd Jega, inda ta bayyana musu cewa daga cikin ayyukan ma’aikatarta akwai magance sababin dake janyo ibtila’I, takaitashi da kuma kulawa da wadanda ya shafa.

Ministar ta jaddada cewa ma’aikatarta za ta inganta tare da karfafa ayyukan jinkai da kuma na bada agaji a tsakanin masu ruwa da tsaki. Kasafin kudin ma’aikatar bada agajin ya kunshi N464,306,285 na kula da ma’aikata, miliyan N165 don sake tsugunar da yan gudun hijirar Borno da Bakassi.

Naira miliyan 15 don shigar da yan gudun hijira 1000 tsarin inshoran lafiya, NHIS, N60m kudin mayar da yan gudun hijira makaranta, N105m don samar da famfunan ruwa, N184m don sayen filayen da za’a tsugunar da yan gudun hijira a Abuja da Nasarawa, N100m kudin tallafi ga mutanen da suka koma garuruwansu a Arewa maso gabas da dai sauransu.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin, ya bayyana farin cikinsa da kasafin, inda yace yana sa ran zai amfani yan Najeriya matuka. Haka nan ya jinjina ma shugaba Buhari daya kirkiri wannan ma’aikata domin ta kula da matsalolin yan gudun hijira da ake fama dasu a Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel