Wata sabuwa: Kasar Saudiyya ta cire dokar zuwa aikin Hajji da muharrami ga mata

Wata sabuwa: Kasar Saudiyya ta cire dokar zuwa aikin Hajji da muharrami ga mata

- Wani sabon al'amari dake neman faruwa a kasar Saudiyya a wannan lokacin shine yadda kasar ta ke neman cire dokar zuwa aikin Hajji ga mata da muharrami

- Kowa dai ya san cewa bai halatta mace wacce take da shekaru kasa da 45 ba ta tafi aikin Hajji ko Umrah ba tare da muharrami namiji ba

- Yanzu haka dai hukumar aikin Hajji da Umrah ta kasar ta fara shirin cire wannan dokar, inda za ta canja dokokin a jikin Visa da za ta bawa mutane masu zuwa ziyara kasar

Kamar yadda kowanne Musulmi ya sani, wajibi ne ga mace wacce ke son zuwa aikin Hajji ta tafi da namiji muharraminta. Inda aka cire wannan dokar akan mata masu shekara 45 zuwa sama sune kawai za su iya zuwa aikin Hajjin ba tare da muharrami ba.

Sai dai kuma a halin yanzu wasu dokoki da kasar Saudiyya ta sanya akan wadanda za ta bawa Visa ta shiga kasar akwai yiwuwar za a cire wannan doka ta zuwa kasar da muharrami ga kowacce mace da take da niyyar zuwa.

KU KARANTA: An gano wani Otel da maza ke zuwa suyi zina da 'yammata su biyansu N500 a wata jihar Najeriya

Yanzu haka hukumar aikin Hajji da Umrah ta kasar tana gabatar da wani bincike da za ta baiwa kowacce mace damar shiga wannan kasar tayi aikin Hajji ba tare da wani muharrami namiji ba.

Sai dai kuma Ministan aikin Hajji da Umrah, Hatim Qadi ya bayyana cewa ba hurumin hukumar aikin Hajji da Umrah bane ta cire wannan doka ta zuwa aikin Hajji da muharrami. Inda ya bayyana cewa ma'aikatarshi ba za ta cire wannan doka ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel