Alkalai sun yi watsi da karar ‘Dan takarar Jam’iyyar adawa, Owuru ya shigar

Alkalai sun yi watsi da karar ‘Dan takarar Jam’iyyar adawa, Owuru ya shigar

- Shugaba Buhari ya sake lallasa ‘Dan takarar HDP, Ambrose Owuru, a gaban Kotu

- Kotun koli sun ba shugaban kasar gaskiya a shari’ar da aka yi kan tazarcensa

A jiya Ranar Litinin, 28 ga Watan Oktoba, 2019, Alkalan babban kotun koli na Najeriya su ka yi wurgi da karar da ‘dan takarar jam’iyyar adawa ta HDP, ya shigar a kan Muhammadu Buhari.

Kotu ta saurari karar da Ambrose Owuru na Hope Democratic Party ya shigar inda a karshe ta yi fatali da karar. Owuru ya na so ne kotu ta soke nasarar da shugaban kasar ya samu a zaben 2019.

Kamar yadda mu ka samu labari, Alkalan da su ka saurari wannan shari’a a karkashin Mai shari’a Olukayode Ariwoola sun watsar da karar kamar yadda kotun daukaka kara ta yi a kwanaki.

KU KARANTA: Kotun koli ta soke wani kara da Atiku da PDP su ka shigar

Olukayode Ariwoola da sauran Alkalai uku da aka kawo karar a gabansu sun bayyana cewa an tafka kura-kurai iri-iri wajen shigar da karar. Shari’ar dai ta kare ne cikin wani irin yanayi a jiya.

Lauyoyin mai tuhuma sun yi kuskuren shigar da kara biyu a lokaci guda. Wannan ya saba doka amma da farko Lauyoyin su ka roki a sake dawo da karar. Daga karshe dai su ka hakura da karar.

Wadannan Lauyoyi ta bakin Sunday Ezeme sun bukaci kotu ta kakkabe korafin na su ta sake dubawa ne amma Lauya Wole Olanipekun wanda ke kare shugaban kasa ya nuna bai yarda ba.

Lauyoyin INEC da APC sun yi na’am da abin da Olanipekun ya fada na cewa za a batawa kotu lokaci ne kurum. A karshe dai an sake fatali da karar kamar yadda Alkali Mary Odili ta yi a da.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel