Barawon da yaje sata ya manta da abinda zai sata bayan mata da miji sun dauke mishi hankali a lokacin da suke jima'i

Barawon da yaje sata ya manta da abinda zai sata bayan mata da miji sun dauke mishi hankali a lokacin da suke jima'i

- Wani kasurgumin barawo da yaje wani gida yin sata ya manta da maganar satar bayan mata da miji sun dauke masa hankali lokacin da suke jima'i

- Mata da mijin sun fito sun iske shi a kwance har bacci ya dauke shi a dakin bayan sun kammala abinda suke yi

- Yanzu haka dai yana hannun jami'an 'yan sanda na jihar Legas, inda suka mika shi ga kotu domin yanke masa hukunci

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kama wani barawo dan shekara 25, wanda ya manta da maganar satar da yaje yi ya koma kallon mata da miji suna jima'i a cikin daki a wani gida dake kan Innocent Amadi Street (Mercy Estate) Ipaja a cikin jihar Legas.

Barawon wanda aka bayyana sunanshi da Uchenna Ebube yayi bacci a lokacin da yake kallon ma'auratan hakan yasa aka yi nasarar kama shi bayan mutumin mai suna Mr. Idris Olumo da matarshi sun gama jima'i suka ganshi a cikin dakin su da misalin karfe 4 na dare.

Bayan an bincike shi, Uchenna ya ce yaje gidan ma'auratan nen domin ya saci wani abu mai tsada, inda ya samu ya shiga ta tagar gidan.

KU KARANTA: Sarakuna sun roki shugaba Buhari ya bari Nnamdi Kanu ya shigo Najeriya don halartar jana'izar mahaifiyarsa

Bayan gurfanar da shi a kotun majistire dake Ejigbo, alkalin da yake shari'a a kanshi Mr. T.O Shomade ya bayar da belin shi akan kudi naira dubu dari da kuma mutane biyu wadanda za su tsaya masa.

Mr. T.O Shomade, ya daga sauraron karar har zuwa ranar 13 ga watan Nuwambar wannan shekarar, inda kuma ya umarci a cigaba da tsare mutumin a gidan yari har zuwa lokacin da zai kammala sharudan belin shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel