Yanzu-yanzu: Buhari ya dira Saudiyya (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Buhari ya dira Saudiyya (Bidiyo)

Jirgin shugaba Muhammadu Buhari ya dira babban filin jirgin saman Sarki Khalid dake birnin Jidda da daren nan.

A yau Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bar Abuja zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar wani taro na masu saka hannu jari (FII) da hukumar samar da kudaden kasuwanci ta kasar Saudiyyya (PIF) ta shirya.

Za a fara taron ne daga ranar 29 ga wata zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, kuma za a tattauna ne a kan harkokin bunkasa kasuwanci ta hanyar fasahar zamani.

Taron na kwana uku za a yi shine a karkashin shugabancin yariman kasar Saudiyya, Mohammed bin Salman Abdulaziz, yayin da sarkin kasar Saudiyya, Salman bin Abduaziz, zai kasance mai masaukin baki.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar gwamnan Babagana Umara Zulum na jihar Borno, gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi da gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

Bayan kammala taron da masu saka hannu jari a birnin Riyadh, shugaba Buhari zai zarce zuwa Makkah domin yin aikin Umrah.

Bayan halartan taron karfafa tattalin arziki a Saudiyya, shugaba Muhamadu Buhari zai garzaya kasar Ingila da sunan ziyarar kansa, imma hutawa ko jinya, kamar yadda yayi a baya.

Buhari ba zai dawo Najeriya ba sai ya kwashe makonni biyu a birnin Landan, zai dawo ranar 17 ga Nuwamba, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel