Najeriya ta zo na 1 a kasashe mafi 'ba haya' a bainar jama'a

Najeriya ta zo na 1 a kasashe mafi 'ba haya' a bainar jama'a

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa Najeriya ta tserewa dukkan kasashen duniya a yawan masu ba haya a bainar jama'a.

Ministan arzikin ruwa, Suleiman Adamu, ya bayyana hakan ne a wani taron kwana biyu kan tsafta a ranar Litinin, 28 ga Oktoba a birnin tarayya Abuja.

A ranar 2 ga watan Oktoba, Najeriya ta kwace matsayin na daya daga hannun Indiya na yawan mutane masu ba haya a fili.

Duk a yau, ministan ya bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa kan arzikin ruwa domin kare kudin da suka bukata a kasafin kudin 2020.

Minista Suleiman Adamu, ya ce kananan hukumomi 14 cikin 774 na kasar nan ne kawai ba'a ba haya a fili.

Ya bayyana cewa yankin Arewa maso tsakiya ne suka fi kowani yanki wajen aikata wannan abu.

Yace: "A yanzu haka, kananan hukumomi 14 a kasar nan ne ba'a 'ba haya' a fili. Akwai dubunnan mutane marasa ban daki."

"Yawancin unguwannin da ake haka na yankin Arewa maso tsakiyar Najeriya."

Sauran kasashe bayan Najeriya da Indiya sune:

Ethiopia (3rd),

Indonesia (4th)

Pakistan (5th)

China (6th)

Niger (7th),

Sudan (8th)

Chad (9th)

Mozambique (10th).

Asali: Legit.ng

Online view pixel