IPPIS: Kungiyar ASUU ta fara barazanar daina zuwa aiki kan albashi

IPPIS: Kungiyar ASUU ta fara barazanar daina zuwa aiki kan albashi

Kungiyar malaman makarantun jami’a na ASUU na reshen Ibadan su na barazanar yi wa gwamnatin tarayya yajin aiki muddi aka ki biyansu albashin karshen wannan watan na Oktoba.

ASUU ta bayyana cewa za ta yi wannan ne domin jaddada rashin goyon bayanta ga shiga tsarin nan na IPIPIS da gwamnatin tarayya ta ke kokarin kakaba ‘ya ‘yanta a ciki da karfi da yaji.

Reshen kungiyar ASUU na Ibadan ya kunshi Jami’ar Ibadan watau UI da kuma jami’ar fasaha ta Ladoke Akintola da ke Osun. Jami’ar jihar Kwara wanda aka fi sani da KWASU ta na cikinsu.

Malaman makarantar sun nuna cewa za su daina aiki muddin aka dakatar da albashinsu. Malaman sun yi wannan jawabi ne ta bakin shugaban ASUU na shiyyar Ibadan, Dr. Ade Adejumo.

KU KARANTA: Gwamnati ta na shirin dauko hayar Likitoci daga ketare

Adejumo ya bayyana cewa shirin da ake yi na jefa Malaman jami’o’i cikin IPPIS wani yunkuri ne na kawo sabon tsarin kudi a makarantun gwamnatin Najeriya wanda sam ba su yarda da shi ba.

Kungiyar ta ASUU ta bayyana wannan matsaya ne a lokacin da shugaban na ta ya zanta da Manema labarai a jam’ar UI da ke babban birnin jihar Oyo a Ranar Lahadi, 27 ga Watan Oktoba.

"A baya mun kasance tare da gwamnati kan koken da kungiyar mu ta gabatar ta bakin wakilanmu a tattaunawar da mu kayi, sai dai da alamu kukan na mu, sun fita ne ta kunnuwansu."

"Gwamnatin ta dage wajen yi wa kungiyarmu furofaganda kuma ana kokarin yi wa ‘ya ‘yan kungiyarmu kisan mummuke," inji Adejumo inda ya kara da cewa IPIPS tsarin cutar jama’a ne.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel