Badakalar kudin wutan lantarkin Najeriya: EFCC ta damke mutane 50

Badakalar kudin wutan lantarkin Najeriya: EFCC ta damke mutane 50

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta damke mutane 50 cikin binciken da take gudanarwa kan yadda aka yi facaka da kudi dala biyan tara na gyaran wutan lantarkin Najeriya.

Za ku tuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya lashi takobin binciken yadda gwamnatocin baya sukayi ikirarin kashe $16bn kan wutan lantarki amma har yanzu babu wuta.

Daga cikin mutanen da aka damke akwai yan kwangila, manyan jami'an gwamnati, Sakatarorin dindindin, ma'aikatan kamfanin lantarkin Neja Delta NDPHC da jami'an TCN.

Sabon bincike ya nuna yadda wasu yan kwangila da ma'aikatan NDPHC suka yi babakere kan $8.5billion na wuta.

KARANTA Yanzu-yanzu: Buhari ya dira Saudiyya (Bidiyo)

Yan kwangila za su amshi kudin aiki ba tare da yin aikin yayinda ma'aikatan NDPHC suke handamar kudaden da aka shiryawa mazauna wuraren da ake shirin kafa tashan wuta.

A yanzu, EFCC ta gano an turawa wani jami'in NDPHC N1.5billion.

A cewar majiya, mutumin yana rokon jami'an EFCC inda ya bayyana sunayen manyan diraktocin kamfanin da suka ci kudin tare.

Bayan haka, EFCC ta damke ma'aikatan wasu kamfanin uku da ake bincike kan lamarin.

Kamfanonin sune Pivot Engineering Company Limited, Hiquado Limited and Chris-Ejik International Agencies Limited.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel