Da dumi dumi: Fursunoni 200 sun tsere daga Kurkukun Kogi sakamakon ambaliyan ruwa

Da dumi dumi: Fursunoni 200 sun tsere daga Kurkukun Kogi sakamakon ambaliyan ruwa

Wani mamakon ruwan sama daya sauka a ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba a jahar Kogi ya lalata gidan yarin garin Koton-karfe wanda hakan ya yi sanadiyyar tserewar fursunoni 200 daga kurkukun, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ruwan ya yi sanadiyyar faduwar gine ginen da fursunonin suke zama a cikinsu yayin daya shanye gidaje da dama a garin, sai dai wani rahoto ya nuna cewa a yanzu haka jami’an tsaro sun sake kama fursunoni 100, yayin da wasu kuma suka dawo da kansu.

KU KARANTA: Buratai ya bayyana bukatar karin kudaden aiki domin yaki da Boko Haram

Majiyarmu ta bayyana cewa tun da misalin karfe 2 na dare ne aka fara ruwan har zuwa safiyar Litinin, wanda hakan ya yi sanadiyyar ambaliyan ruwa daga rafin Osugu kamar yadda limamin babban Masallacin Koton-Karfe, Saidu Sulaiman ya bayyana.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yin a jin ta bakin gandurobobin dake gidan yarin ya ci tura, sakamakon sun ki amincewa su yi magana ga yan jaridu game da aukuwar lamarin. Haka nan koda wakilin majiyarmu ya ziyarci ofishin shugaban kurkukun, bata tarar da kowa a wajen ba.

A wani labari kuma, al’ummar unguwar Hayin Malam Bello sun shiga cikin halin jimami biyo bayan mamakon ruwan sama da ya sauka wanda ya yi awon gaba da wata babur din keke Napep dake dauke da fasinjoji har ya yi sanadiyyar mutuwar wata budurwa.

Lamari ya faru ne da yammacin Lahadi, 27 ga watan Oktoba a Hayin Malam Bello dake yankin Rigasa na karamar hukumar Igabi ta jahar Kaduna, ruwan sama ya mamaye gadar shiga cikin unguwar ta Hayin Malam Bello.

Amma a haka wani direban Keke Napep ya kutsa kai kan gadar da nufin kokarin hayewa duk da karfin ruwan dake wucewa kan gadar, a dalilin haka ruwan ya tafi da babur din zuwa cikin rafi, inda ruwan ya yi awon gaba da mata biyu dake cikin babur din.

Jama’a sun yi kokarin ceto direban babur din, tare da mace guda, amma ruwan ya yi awon gaba da wannan budurwa mai suna Balaraba, wanda aurenta bai wuce kwanaki 5 ba, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel