Yadda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kashe mutum 7 a Saudiyya

Yadda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kashe mutum 7 a Saudiyya

Akalla mutane bakwai ne suka gamu da ajalinsu a yankin gabashin kasar Saudiyya sakamakon mamakon ruwan sama daya sauka a yankin, kamar yadda hukumar tsaron ta farin kaya na kasar Saudi Arabia ta bayyana.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito wannan ruwan sama ya sauka ne a yankin Hafar Al-Batin, inda ya yi ta kwarara tun daga ranar Juma’a har zuwa ranar Lahadi, kamar yadda kaakakin hukumar tsaron farin kaya na kasar ya tabbatar.

KU KARANTA: Sabon watan Musulunci: Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmai su nemi watan Rabiul Awwal

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin hukumar ya kara da cewa ta samu nasarar tseratar da mutane 16 yayin da ta tsugunar da mutane bakwai, amma ruwan ya lalata motoci guda 40.

A wani labari kuma, al’ummar unguwar Hayin Malam Bello sun shiga cikin halin jimami biyo bayan mamakon ruwan sama da ya sauka wanda ya yi awon gaba da wata babur din keke Napep dake dauke da fasinjoji har ya yi sanadiyyar mutuwar wata budurwa.

Lamari ya faru ne da yammacin Lahadi, 27 ga watan Oktoba a Hayin Malam Bello dake yankin Rigasa na karamar hukumar Igabi ta jahar Kaduna, ruwan sama ya mamaye gadar shiga cikin unguwar ta Hayin Malam Bello.

Amma a haka wani direban Keke Napep ya kutsa kai kan gadar da nufin kokarin hayewa duk da karfin ruwan dake wucewa kan gadar, a dalilin haka ruwan ya tafi da babur din zuwa cikin rafi, inda ruwan ya yi awon gaba da mata biyu dake cikin babur din.

Jama’a sun yi kokarin ceto direban babur din, tare da mace guda, amma ruwan ya yi awon gaba da wannan budurwa mai suna Balaraba, wanda aurenta bai wuce kwanaki 5 ba, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel