An gano abinda yasa Buhari zai wuce kasar Ingila daga Saudiyya

An gano abinda yasa Buhari zai wuce kasar Ingila daga Saudiyya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai shafe kusan kwanaki 16 a kasar Ingila bayan ya kammala ziyarar aiki da aikin Umrah a kasar Saudiyya, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.

An dade ana gunaguni a kan yawan ziyarar da Buhari ke kai wa kasar Ingila da sunan hutu ko kuma duba lafiyarsa.

Jaridar SaharaReporters ta wallafa cewa tun a shekarar 2017 likitoci a kasar Ingila suka tabbatar mata da cewa shugaba Buhari na fama da cuta a cikin cikinsa da ake kira da 'Crohn's disease'.

A ranar Litinin ne fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa shugaba Buhari zai wuce kasar Ingila bayan ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki uku da kuma aikin Umrah a kasar Saudiyya.

Duk da fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Buhari zai wuce kasar Ingila ne domin ya huta sakamakon gajiyar da ya yi daga yawan aiki, SaharaReporters ta ce an boye gaskiyar abinda yasa Buhari zai ziyarci kasar Ingila.

DUBA WANNAN: Buhari ya tafi kasar Saudiyya tare da gwamnonin arewa 3 da ministoci 7 da wasu sauran hadimai

SaharaReporters ta bayyana cewa an taba cire wa Buhari wani bangare na hanjin cikinsa a shekarar 2013, sannan kuma an kara yi masa wani aikin a shekarar 2016 yayin daya daga cikin ziyarar sirri da ya kai kasar.

'Yan Najeriya da dama na yawan yin tambayar daga ina ake samar da kudaden da Buhari ke amfani da su domin daukar nauyin bulaguron da yake yawan yi zuwa kasashen ketare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel