Buratai ya bayyana bukatar karin kudaden aiki domin yaki da Boko Haram

Buratai ya bayyana bukatar karin kudaden aiki domin yaki da Boko Haram

Babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana bukatar gwamnati ta sake zuba kudade a yakin da Sojoji suke yi da ta’addanci domin samun daman fuskantar kalubalen tsaron yadda ya kamata.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito Buratai ya bayyana haka ne a yayin wani taron horas da jami’an sashin kudi na rundunar Sojan kasa daya gudana a garin Uyo na jahar Akwa Ibom a ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Sabon watan Musulunci: Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmai su nemi watan Rabiul Awwal

Buratai wanda ya samu wakilcin babban kwamanda shiyya ta 6 na rundunar Sojan kasa, Jamil Sarham ya bayyana cewa rundunar Sojan kasa na fama da karancin kudade idan aka duba girman ayyukan tabbatar da tsaro da take yi, da kuma matsalolin tsaron dake kasar.

Sai dai Buratai ya tabbatar da cewa sabbin tsare tsare da dokokin da gwamnati ta kirkiro a fannin kudi na kasar nan ya taimaka wajen rage sata da barnatar da kudade a rundunar Sojan, wasu daga cikin tsare tsaren sun hada da asusun bai daya, TSA da kuma IPPIS.

“Wadannan tsare tsaren zasu taimaka wajen tabbatar da rundunar ta kashe kudadenta yadda ya kamata, saboda haka na kafa sashin bincike da gudanar da kudadenmu, DAFM, wanda take kai min rahoton ayyukanta kai tsaye.” Inji shi.

Daga karshe Buratai ya yi kira ga Sojoji dasu tabbata sun kasance masu biyayya ga gwamnatin Najeriya, sa’annan su zamto masu biyayya ga dokokin kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel