Har ila yau: Kotun koli ta sake yin watsi da karar kalubalantar nasarar Buhari

Har ila yau: Kotun koli ta sake yin watsi da karar kalubalantar nasarar Buhari

A ranar Litinin ne kotun koli koli ta sake yin watsi da daukaka karar kalubalantar sake zaben Buhari da dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar HDP, Ambrose Owuru, ya shigar.

Owuru na neman kotu ta soke nasarar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa Buhari ya samu a zaben 2019.

Kotun, mai alkalai hudu, a karkashin jagorancin mai shari'a, Jastis Olukayode Ariwoola, ta yi watsi da karar ne biyo bayan janyewar da masu kara suka yi.

Mista Owuru da jam'iyyarsa sun nemi kotun ta basu izinin sake gabatar da karar farko da suka shigar, wacce aka samu kuskure a cikinta.

Lauyan da ke wakiltar Mista Owuru, Sunday Ezema, ya bawa jama'a mamaki bayan ya yi mi'ara koma baya, watau ya bayyana cewa sun janye karar da suka daukaka.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Jami'an EFCC sun kama 'Magu' na bogi yana kokarin damfarar wasu manyan jami'an gwamnati

Lauyan ya bayyana janyewarsu daga karar ne bayan kotu ta tambaye shi ko za a iya sauraron karar da suka shigar duk da an samu kura-kurai a cikinta, amma maimakon ya bayar da cikakken bayani bayan ya amsa cewa 'Eh', sai kawai ya bayyana cewa sun janye karar.

A wani takaitaccen hukunci da Jastis Ariwoola ya zartar, ya bayyana cewa kotun ta yi watsi da karar.

Tun da farko, lauyan da yake kare shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Wole Olanipekun, ya kalubalanci bukatar masu kara na neman a sake sauraren karar da suka shigar ta farko, wacce kuma aka samu kura-kurai a cikinta, inda ya bayyana cewa babu isashen lokacin da za a yi hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel