'Yan bindiga sun kashe Liman, sun yi awon gaba da mutane da yawa a Jalingo

'Yan bindiga sun kashe Liman, sun yi awon gaba da mutane da yawa a Jalingo

Wani limami mazaunin Jalingo, Malam Gambo tare da wani mutum daya sun rasa rayukansu sakamakon harin da wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai.

'Yan bindigar sun kara da yin awon gaba da mutane masu yawa. Jaridat Daily Trust ta gano cewa, lamarin ya auku ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar lahadi kusa da kauyen Sibire dake kan titin Jalingo zuwa Mutumbiyu.

An kara ganowa cewa, mutanen biyu da suka rasa rayukansu suna dawowa ne daga gona inda suka hadu da 'yan bindigar. Daya daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindigar, Ibrahim Nuhu, ya sanar da jaridar Daily Trust cewa, 'yan bindigar sun tare titi ne tare da harbin duk wata mota mai zuwa ko komawa.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Jami'an EFCC sun kama 'Magu' na bogi yana kokarin damfarar wasu manyan jami'an gwamnati

Yace wasu 'yan kauyen ne suka tsayar dashi tare da sanar masa 'yan bindiga sun rufe hanyar.

Ibrahim ya ce, 'yan bindigar sun kwashi mutane sunyi cikin daji dasu amma jami'an 'yan sanda sun tseratar dasu.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya tabbatar da kisan mutane biyun tare da tseratar da mutane biyun da jami'an 'yan sandan suka yi.

Hakazalika Misal ya ce bai tabbatar da garkuwa da wasu mutanen da 'yan bindigar suka yi ba a titin Jalingon zuwa Mutumbiyu. A halin yanzu titin ya kasaance tashin hankulan masu ababen hawa saboda yawaitar sace mutane da akeyi a titin.

Tuni dai an tura mafarauta cikin dajin don su taimaka wajen zakulo masu garkuwa da mutanen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel