Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da sufeton dan sanda da wani mutum guda a garin Abuja

Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da sufeton dan sanda da wani mutum guda a garin Abuja

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun yi garkuwa da wani sufeton dan sandan mai suna Selven da kuma wani Nengba Mundi a garin Rubochi da ke yankin Kuje a babbar birnin tarayya, Abuja.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an sace mazajen biyu ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba, sa’o’i 48 bayan ya bindiga sun sace kanin wani tsohon shugaban karamar hukumar Kuje, Mohammed Galadima, a wannan garin.

An tattao cewa masu garkuwa da mutanen sun kai mamaya garin su da yawa a tsakar dare inda suke ta harbi ba kakkautawa.

Mataimakin kakakin yan sandan birnin tarayya, ASP Mirriam Yusuf, ta yi alkawarin samar da cikakken bayani kan lamarin daga baya.

KU KARANTA KUMA: Ana saura kwana 5 auranta ruwa ya yi awon gaba da ita (hotuna)

A wani labarin kuma mun ji cewa sojojin kasar Najeriya sun tabbatar da cewa Jami’ansu sun kai wani hari a inda Miyagun da su ka addabi jama’a a jihar Kaduna su ke boye.

Wani babban Jami’in yada labarai na gidan Sojan kasa, Kanal Aminu Iliyasu, ya fitar da jawabi inda ya bayyana cewa Dakarun Runduna ta 342 sun kai samame a inda wasu Miyagu su ke boye.

Aminu Iliyasu yace Dakarun na su sun farma wadanda ake zargi su na garkuwa da mutane ne a Garin Ihie a cikin karamar hukumar Ohaji/Egbema da ke jihar Imo inda aka damke mutane biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel