Yanzu-yanzu: Gobara ta lashe wani sashen hedkwatan FIRS dake Abuja

Yanzu-yanzu: Gobara ta lashe wani sashen hedkwatan FIRS dake Abuja

Wata gobara ya tashi a hedkwatan hukumar karban haraji ta kasa wato FIRS dake birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, Premium Times ta ruwaito.

Wutar ta lakume wani dakin ajiya dake jikin dakin cin abincin ma'aikatan hukumar a hedkwatan.

Kakakin hukumar, Wahab Gbadamosi, ya bayyanawa manema labarai cewa "wata karamar gobara ya kona dakin ajiyar FIRS dake kusa da wajen cin abinci."

"Jami'an kwana-kwanan da suka kashe wutan suna gudanar da bincike kan abinda ya janyo gobarar."

Yanzu-yanzu: Gobara ya lashe wani sashen hedkwatan FIRS dake Abuja
hedkwatan FIRS dake Abuja
Asali: UGC

A wani labarin daban, wani babban ma’aikacin kamfanin sarrafa abinci na Sweet Sensation, kuma jami’in kula da asusun kamfanin, Mista Michael Thadius ya yi awon gaba da kimanin N1,400,000 daga asusun kamfanin sa’annan ya banka ma ofishin nasa wuta, ya buga ma wandonsa iska.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito jami’in rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas mai shigar da kara, Sajan Felicia Okwori ce ta bayyana haka ga Alkalin kotun majistri dake zamanta a Ikejan jahar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel