2023: Bakare ya yiwa wasu manyan yan siyasa wankin babban bargo

2023: Bakare ya yiwa wasu manyan yan siyasa wankin babban bargo

- Shugaban cocin Latter Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare ya caccaki wasu yan siyasa da ya bayyana a matsayin sakakkarun dake sa ran zama shugabannin kasa a 2023

- Faston ya kuma gargadi wasu da ya zarga da hamdame kudin jama'a da yawo a jirage masu zaman kansu, inda ya sha alwashin cewa wata rana sai sun amayar da kudaden da suka sata

- Bakare ya kuma soki gwamnatin jihar Lagas akan rashin gyara hanyoyi a jihar tun 1999

Shugaban cocin Latter Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare, a jiya Lahadi, 27 ga watan Oktoba ya yi ba a ga wadanda ya bayyana a matsayin sakakkarun dake sa ran zama shugabannin kasa a 2023, inda yace lallai ba za su yi nasara ba saboda sun sace abunda yake mallakin mutane.

Faston ya kuma gargadi wasu mutane da bai ambaci sunayensu ba dake zaune a babban birnin Ikoyi a Lagas, wadanda ya zarga da hamdame kudin jama'a da yawo a jirage masu zaman kansu, inda ya sha alwashin cewa wata rana sai sun amayar da kudaden da suka sata.

Ya zargi gwamnatin jihar Lagas da rashin gyara hanyoyi a jihar tun 1999.

KU KARANTA KUMA: Action Aid ta ce a rage albashin da ake biyan masu mukami da ‘Yan Majalisun Tarayya

A cewar The Cable, Bakare ya fadi hakan ne a lokacin wani wa’azi a cocin Latter Rain Assembly.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel