Kwangilar N9.5b: Stella Oduah ta yi awon gaba da kudin tsaron filin jirgi - EFCC

Kwangilar N9.5b: Stella Oduah ta yi awon gaba da kudin tsaron filin jirgi - EFCC

A lokacin Sanaata Stella Oduah ta kujerar Minista, ta karkatar wasu daga cikin Naira biliyan 9.5 da aka ware domin sayen kayan tsaro a filayen sauka da tashin jirgin saman Najeriya, inji EFCC.

Hukumar mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta ce Stella Oduah ta wawuri wadannan kudi ne a lokacin da ta ke rike da ta ke Ministan harkokin jirgin saman kasar.

EFCC ta gabatar da wannan ne a cikin hujjojin ta na maka tsohuwar Ministar kara a gaban kotu. Tun kwanakin baya ne EFCC ta shigar da Sanata Oduah kara a gaban wani kotun tarayya a Abuja.

Kawo yanzu dai EFCC ta samu nasarar karbe kayan da Sanatar ta saya da kudin da ake zargin ta sata daga asusun gwamnati. Alkalink Kotu ya bada iznin fara rike wannan kaya na wucin-gadi.

KU KARANTA: APC ta jefa kalubale bayan an kai korafin Bola Tinubu gaban EFCC

Tsakanin 2012 zuwa shekarar 2014, lokacin da Stella Oduah ta ke Ministar tarayya, ta hada baki da bankuna wajen yin awon-gaba da kudin da ta bada na sayo kayan sa-ido a filayen jirgin sama.

Daga cikin abubuwan da aka ware za a saya akwai kayan talabijin da kuma wasu kaya masu tsada. A hujjojin da EFCC ta bada, ta bayyana cewa Oduah ta yi gaba da wasu kudin kwangilar.

Wasu daga cikin kayan da aka iya saya su na jibge a Garuruwan Bayelsa, Ribas da babban birnin tarayya Abuja. Yanzu ana zargin Sanatar da sata, da facaka da dukiya da cogen kwangila.

EFCC ta fara samun korafi ne daga hannun jama’a kafin ta binciki tsohuwar Ministar kasar. Oduah ta ba kamfanin I-Sec Security kwangilar shigo da na’urorin tsaro ne a filayen jirgi 22 na kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel