Wani mutumi ya kar ‘yar shi har lahira bayan ya buga kanta da kasa

Wani mutumi ya kar ‘yar shi har lahira bayan ya buga kanta da kasa

- Yan sanda sun kama wani magidanci mai suna Isiaka Ayobami, kan zargin kashe yar shekara daya

- Abayomi ya fizge yar tasa ne daga hannun mahaifiyarta sannan ta rotsa kanta da kasa

- Kakakin yan sandan jihar Lagas ya ce za a tuhumi mutumin da laifin kisan kai

Jami’an yan sanda a jihar Lagas sun kama wani magidanci mai suna Isiaka Ayobami, kan zargin kashe wata yarinya yar shekara daya da haihuwa.

Bala Elkana, kakakin yan sandan jihar ya bayyana cewa "a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba, wani Alhaji Garruba Isiaka wanda ke a gida mai lamba 7 unguwar Ayo Ijaiye ya kai kara ofishin yan sanda da misalin karfe 6:00 na yamma cewa yayinda yake a Berger, ya amsa kiran waya daga kaninsa, Alhaji Mohammed Isiaka, cewa mai laifin wanda ke zama a gida mai lamba 2 unguwar Ayo Ijaiye Isheri, ya fisgi yarsa mai shekara daya wacce ake kira Nana Aishat Isiaka daga hannun mahaifiyarta sannan ya buga ta da kasa."

Bala yace kan yarinyar ya dagargaje sannan anan take ta mutu.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai tafi Saudiyya tare da gwamnoni 3 da ministoci 7 da wasu sauran hadimai

Fusatattun matasa daga yankin sun so lallasa mai laifin, idan ba don yan sanda da suka yi gaggawan shiga tsakani ba.

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa za a tuhume shi da laifin kisan kai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel