Inyamurai sun fara hada-kai da nufin fito da Shugaban kasa a zabe mai zuwa

Inyamurai sun fara hada-kai da nufin fito da Shugaban kasa a zabe mai zuwa

- Jagororin Kabilar Ibo sun dage a kan batun samun mulkin kasa a 2023

- Shugabannin Yankin sun fara kokarin hada-kai domin cin ma nasara

- Ana kokarin jawo duka Attajirai da Sarakuna da ‘Yan siyasar Yankin

Mun samu rahoto daga Jaridar The Telegraph cewa mutanen Kudu maso Gabas sun fara harin mulkin Najeriya a shekarar 2023 gadan-gadan inda su ke ta shirya taro iri-iri domin su kai labari.

Manyan ‘yan boko da ‘yan siyasa da kuma Attajirai da ‘ya kasuwa da Sarakunan gargajiyan yankin su na halartar wannan taro da ake yi a gidan wani tsohon gwamna kamar yadda mu ka ji.

Yunkurin da ake yi shi ne ayi watsi da duk wani banbancin siyasa a ba Inyamuri tuta a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 kamar yadda PDP da AD su ka tsaida Yarbawa a 1999.

KU KARANTA: Mutanen Ibo su fara hangen kujerar Shugaban kasa bayan Buhari

Wani ‘dan majalisar yankin, Honarabul Benjamin Kalu ya bayyana cewa da gaske su ke harin shugaban kasa a 2023. ‘Dan majalisar tarayyar ya ce ya kamata a ba kowace kabila damar mulki.

An rahoto Kalu ya na cewa: “Mun fi karfi idan mu ka hada kai idan har mu na so mu karbi kujerar farko a kasar.” Dan majalisar yace za a fi samun zaman lafiya idan kowane yanki ya yi mulki.

Jita-jitar da ke yawo shi ne wani Mai kudi a shiyyar Kudu maso Gabashin kasar zai saki makudan kudi saboda ganin mulkin Najeriya ya koma hannun Ibo, abin da ba a taba yi ba a farar hula.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel