Yakin neman zabe: "Zuma" sun tarwatsa dandazon magoya bayan PDP a Kogi, jama'a sun kaurace wa wurin taron

Yakin neman zabe: "Zuma" sun tarwatsa dandazon magoya bayan PDP a Kogi, jama'a sun kaurace wa wurin taron

Sa'o'i kadan bayan kaddamar da yakin neman zaben jam'iyyar PDP a zaben gwamnoni na wannan shekarar, zuma suka tarwatsa taron da aka fara a filin wasa na jihar Kogi dake Lokoja.Magoya bayan dan takarar jam'iyyar PDP din sun zargi sa hannun wasu makiyan cigaban su. Sun kuma bayyana cewa, koda wuta za a konasu, suna nan daram akan ra'ayinsu.

Zumar sun harbi wasu daga cikin mutanen inda wasu suka fara neman inda zasu buya.

'Yan jam'iyyar da yawa da suka yi niyyar halartar taron sun canza shawara sakamakon jin mummunan lamarin da ke aukuwa.

Sun koka cewa, a wancan karon 'yan bindiga ne suka taso su gaba yayin zaben fidda gwani. Lamarin ya faru ne a ranar 3 ga watan Augusta na wannan shekarar yayin da suke zaben fidda gwani na jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Mudassir and Brothers: Dan kasuwa zai gina kamfanin atamfa na $50m a Kano

Jaridar Daily Times ta ruwaito cewa, 'yan jam'iyyar PDP da ke jiran isowar dan takararsu Musa Wada tare da manyan shuwagabannin jam'iyyar da wasu gwamnoni sun tarwatse ne sakamakon harin da zumar suka kai musu. Duk da kuwa harin, wasu daga cikin magoya bayan Wada sai da suka kara dawowa tare da jeruwa don jiran isowar tauraron nasu..

Anyi nasarar kaddamar da yakin neman zaben duk da yunkurin hana hakan da zuma suka yi. Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da gwamnonin jihohin Benuwe, Taraba, Bauchi da Sakkwato duk sun samu halartar taron. Dubban magoya bayan jam'iyyar PDP sun cika filin daga baya don nuna goyon baya ga Injiniya Musa Wada.

'Yan gani-kashenin jam'iyyar na jihar Kogi sun bayyana cewa, "Koda za a kona mu da wuta ne, sai mun halarci wannan bikin kaddamar da yakin neman zaben. Duk wanda yayi mana wannan barazanar ya sani, ubangiji na bayanmu. Kuma ba zai yi nasara ba. Muna nan muna goyon bayan dan takararmu Musa Wada."

"An yi amfani da bindiga wancan karon, yanzu kuma an canza salon tarwatsamu. Toh ba zasu yi nasara ba. Ubangiji na tare da mu" cewar wani dan siyasa Saidu Suleman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel