Action Aid ta ce a rage albashin da ake biyan masu mukami da ‘Yan Majalisun Tarayya

Action Aid ta ce a rage albashin da ake biyan masu mukami da ‘Yan Majalisun Tarayya

Mun ji cewa kungiyar nan ta Action Aide Nigeria watau AAN ta yi kira da cewa ayi maza a rage yawan abin da ‘yan majalisun kasar nan su ke tashi da shi a matsayin albashi da alawus a ofis.

Wannan kungiya mai zaman kanta ta na so a rage adadin abin da gwamnati ta ke kashewa a kan masu mulki wadanda su ka hada da ‘yan majalisu da duk wasu masu rike da babban ofis a kasar.

AAN ta ce wannan zai sa a adana kudin da za ayi wa Najeriya ayyukan gina kasa da more rayuwa. Kungiyar ta bayyana wannan ne bayan taron da ta shirya a Ranar Lahadi, 27 ga Oktoba, 2019.

Shugabaar majalisar amintattu watau BOT na wannan kungiya, Dr. Jummai Umar-Ajijola, ita ce ta yi magana a madadin kungiyar a karshen zaman da su ka yi domin duba halin da kasa ta ke ciki.

Jummai Umar-Ajijola ta bukaci gwamnatin kasar ta yi gaggawan rage yawan ma’aikatu da hukumominta. A cewar ta, hakan ya zama dole ganin irin kalubalen da ke tattare kasafin kudi.

KU KARANTA: Buhari zai lula Kasar Saudiyya daga dawowa kasar Turai

Umar-Ajolola ta ke cewa: “Dole gwamnati ta hada kai da hukumar RMFAC domin a rage albashin duka ‘yan majalisu da sauran masu rike da mukamai a Najeriya domin a adana kudin yin ayyuka.”

.“Kudin da ake kashewa wajen tafiyar da mulki a Najeriya ya yi matukar yawa, akwai bukatar daukar matakin gaggawa idan har gwamnati ta na son shawo kan matsalar. Inji Umar-Ajijola.

Kungiyar AAN ta kuma ce akwai gyara a yadda ake karba da kashe harajin kayan masarufi na VAT. Kungiyar ta kuma yi tir da irin makudan kudin da Najeriya ta ke batarwa wajen biyan bashi.

A shawarar ta, AAN ta nemi a soke majalisar wakilai ko kuma majalisar dattawa, sannan tace ya kamata ace an warewa harkar ilmi da kiwon lafiya da gona, kaso mai tsoka a kasafin kudin 2020.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel