A karon farko: Najeriya ta fara dinka ma kafatanin jami’an tsaronta khaki a cikin gida

A karon farko: Najeriya ta fara dinka ma kafatanin jami’an tsaronta khaki a cikin gida

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da katafaren kamfanin da zai dinka ma kafatanin jami’an tsaron Najeriya kayan sawansu, watau Khaki, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnati ta bude wannan kamfani ne domin ta samar da sahihin tsarin hana amfani da khakin Soji da na sauran jami’an tsaro da wasu fararen huluna suke yi, da kuma miyagun mutane.

KU KARANTA: Buhari ya jajanta ma iyalan Tafawa Balewa game da mutuwar uwargidarsa

Daraktan watsa labaru na ma’aikatar cikin gida, Muhammad Manga ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba a babban birnin tarayya Abuja.

A jawabinsa, darakta Muhammad Manga ya bayyana cewa an kaddamar da kamfanin ne a unguwar Kakuri na jahar Kaduna mai suna DICON-SUR Corporate Wears Nigeria Limited, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari yace tsaron Najeriya babban lamari ne ga gwamnatin Najeriya.

“Wannan taro na kaddamar da wannan kamfani ya tabbatar da manufar gwamnatinmu na bayar da kwarin gwiwa ga tsarin alakar kasuwanci tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu ta hanyar zuba jari.” Inji shi.

Shugaba Buhari ya samu wakilcin ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana cewa an samar da wannan kamfani ne sakamakon bukatar samun kamfanin da zata dinka ma jami’an tsaro kayan aiki, sa’annan ya bada tabbacin ba zasu taba lamuntar duk wasu miyagun ayyuka ba.

Haka zalika Buhari yace yana fatan kamfanin zata cimma manufar kafata na daukan ma’aikata 1,000 zuwa shekarar 2021, sa’annan ya kara da cewa za’a dinga samar ma kamfanin auduga daga jahohin Kaduna, Gombe, Katsina, Bauchi da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel