Kogi 2019: Gwmana Yahaya Bello zai kai ga nasara - Inji Osinbajo

Kogi 2019: Gwmana Yahaya Bello zai kai ga nasara - Inji Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole da kuma wasu gwamnonin APC sun kaddamar da yakin neman zabe gwamna a Kogi.

A Ranar Lahadi, Yemi Osinbajo da sauran manyan jam’iyyar APC su ka dura jihar Kogi ne domin soma kamfe na zaben gwamnan da za ayi a watan gobe. Osinbajo ya ba ‘yan takarar APC tuta a gaban jama’a.

Farfesa Osinbajo ya mikawa gwamna mai-ci Yahaya Bello da kuma Abokin takararsa watau Edward Onoja tutar jam’iyyar APC ne inda ya nuna cewa yana na sa ran APC ta kai labari a zaben jihar.

A wajen an ji shugaban APC ya na cewa: “Idan kun san halin da jihar nan ta ke ciki a lokacin mulkin PDP, da kuma yadda ta ke yau, za ku fahimci cewa akwai bukatar a zabi Bello ya cigaba da mulki.”

KU KARANTA: Dalilin da ya sa aka rufe iyakokin kasa - Osinbajo ya yi bayani

A karshen jawabin na sa, Shugaban APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole ya kara da cewa: “Bello ya aiya aiki don haka na ke kira gare ku da ku zabe shi a lokacin zabe kuma ba zai ba ku kunya ba.”

A na sa jawabin, gwamnan ya fadawa taron jama’a cewa su dage wajen ganin sun kai ga nasara. Gwamna Bello ya kuma bayyana cewa APC za ta yi kamfe gida-gida a fadin jihar domin ta zarce a mulki.

Wadanda su ke wurin wannan yawon yakin neman zabe sun hada gwamnoni Abdullahi Sule, Abdulrahman Abdulrazak da Mai Mala Buni, Sani Bello. Sai irin su Salamatu Baiwa da Ramatu Tijjani.

Dazu ku ka ji cewa jam’iyyar PDP ta samu kwarin gwiwa a zaben jihar Bayelsa bayan Goodluck Jonathan ya ajiye banbancinsa yi wa ‘Dan takara Sanata Diri Doueye mubaya’a a zaben sabon gwamna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel