Goodluck Jonathan: Ba zan iya yi wa Jam’iyyar APC aiki a Bayelsa ba

Goodluck Jonathan: Ba zan iya yi wa Jam’iyyar APC aiki a Bayelsa ba

Mun samu labari a karshen makon nan cewa burin jam’iyyar PDP na cigaba da rike jiha Bayelsa ya samu kwarin gwiwa bayan da tsohon shugaba kasa Dr. Goodluck Jonathan ya mara baya.

Bayan wani muhimmin taro da aka yi, Goodluck Jonathan ya nuna cewa zai goyi bayan takarar Sanata Diri Duoye wanda ake tunanin cewa gwamna mai-ci, Seriake Dickson ne ya kawo sa.

An yi zama ne bayan labule tsakanin gwamna Hon. Seriake Dickson da kuma tsohon shugaban kasar a karsshen makon nan. An yi wannan zama ne a gidan tsohon shugaban kasar da ke Abuja.

Wasu daga cikin Gwamnonin jam’iyyar PDP sun halarci wannan taro inda aka ji Jonathan ya na cewa: “Ta ya za ayi in yi wa jam’iyyar APC aiki bayan ina cikin manya kuma uban jam’iyyar PDP?”

KU KARANTA: Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP ya mutu a Birnin Tarayya

Tsohon shugaban Najeriyar ya nuna cewa har gobe yana cikin ‘yan gaban goshin PDP kuma ya bayyana kansa a matsayin Uban jam’iyyar hamayyar yayin da ake wasu jita-jitar ba ya tare da su.

Gwamnonin jihohin da su ka halarci taron na Abuja sun hada da Okezie Ikpeazu; Seyi Makinde; Dave Umahi; Rt, Hon. Aminu Tambuwal; Arch. Darius Ishaku da kuma Sanata Bala Mohammed.

Haka zalika Darekta Janar na kungiyar gwamnonin PDP, Earl Osaro Onaiwu, ya na wajen wannan ganawa da aka yi domin ganin jam’iyyar PDP ta samu nasara a zaben jihar Bayelsa da za ayi.

Jonathan ya nuna cewa zai marawa Douye baya ya kai labari duk da sabaninsa da gwamna Dickson. Jonathan ya na ganin cewa idan APC ta karbe jihar shi ne babban wanda ya ji kunya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel