Babbar magana: Jami'an EFCC sun kama 'Magu' na bogi yana kokarin damfarar wasu manyan jami'an gwamnati

Babbar magana: Jami'an EFCC sun kama 'Magu' na bogi yana kokarin damfarar wasu manyan jami'an gwamnati

Ofishin hukumar yaki da rashawa ta EFCC na yankin Fatakwal, ya sanar da cafke wani mutum da ake zargi da basaja da sunan shugaban hukumar, Ibrahim Magu. An kama mutumin ne yana barazana ga daraktocin hukumar habaka yankin Niger Delta (NDDC).

Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar, ya bayyana hakan ne a wata takarda data fito daga hukumar. Wanda ake zargin mai suna Robert Swem Terfa, ya bukaci cin hanci ne daga jami'an NDDC domin "Kashe zargin rashawa" da ake musu.

DUBA WANNAN: Yakin neman zabe: "Zuma" sun tarwatsa dandazon magoya bayan PDP a Kogi, jama'a sun kaurace wa wurin taron

An cafke Terfa ne a otal din Juanita da ke Fatakwal inda yake taro da daraktocin hukumar NDDC bayan da ya tallata musu "hanyar da zaibi wajen cire sunayensu daga cikin jerin wadanda ake zargi na hukumar".

Wanda ake zargin, ya bayyanawa daraktocin cewa yana wakiltar Magu ne. Ya kara da tabbatar musu da cewa, za a cire sunayensu daga jerin sunayen da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada don bincika a hukumar habaka yankin na Niger Delta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel