Najeriya ta fadi dabarar da za tayi domin dauko likitoci daga kasashen Turai

Najeriya ta fadi dabarar da za tayi domin dauko likitoci daga kasashen Turai

Gwamnatin Najeriya ta shirya dauko likitoci daga kasashen Turai da Amurka domin inganta harkokin kiwon lafiya a kasar kamar yadda ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayar da shaida.

Muryar Duniya ta ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta kudiri aniyar hakan ne a daidai lokacin da mafi akasarin likitocin kasar nan ke aiki a kasashen ketare.

Sanarwar da ma'aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya ta fitar na zuwa ne a daidai lokacin da masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya ke bayyana damuwa a kan yadda ma'aikatan lafiya ke yin kaura daga kasar.

Ministan na lafiya ya ce tuni ma'aikatarsa ta fara tattaunawa da ofisoshin jakadancin kasashen ketare domin zakulo kwararru da za su yi aiki a fannonin lafiya daban-daban a fadin Najeriya.

Sai dai Mista Osagie ya ce ma'aikatar lafiyar za ta bukaci karin kudade domin bude kofar da za ta kwadaitar da kwararrun ma'aikatan lafiya 'yan asalin kasar nan da kuma na kasashen ketare wajen dawo wa aiki a nan gida.

KARANTA KUMA: Ambaliya ta shanye kauyuka 40 a jihar Adamawa

A shekarar 2018, wasu alkalumma sun nuna cewa kwararrun likitoci ‘yan Najeriya, da ma’aikatan jinya sama da dubu 5 ne ke aiki da bangaren lafiya na gwamantin Birtaniya kawai.

Kididdigar alkalumman da aka fitar a shekarar 2018 ta bayyana cewa, kwararrun likitoci 'yan Najeriya da sauran ma'aikatan jinya fiye da dubu biyar ne ke aiki a bangaren lafiya na kasar Birtaniya kadai.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel