Buhari zai tafi Saudiyya tare da gwamnoni 3 da ministoci 7 da wasu sauran hadimai

Buhari zai tafi Saudiyya tare da gwamnoni 3 da ministoci 7 da wasu sauran hadimai

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai bar Abuja zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar wani taro na masu saka hannu jari (FII) da hukumar samar da kudaden kasuwanci ta kasar Saudiyyya (PIF) ta shirya.

Za a fara taron ne daga ranar 29 ga wata zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, kuma za a tattauna ne a kan harkokin bunkasa kasuwanci ta hanyar fasahar zamani.

Taron na kwana uku za a yi shine a karkashin shugabancin yariman kasar Saudiyya, Mohammed bin Salman Abdulaziz, yayin da sarkin kasar Saudiyya, Salman bin Abduaziz, zai kasance mai masaukin baki.

Shugaba Buhari zai samu rakiyar gwamnan Babagana Umara Zulum na jihar Borno, gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi da gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

A cikin tawagar akwai karamin ministan harkokin kasashen waje, Zubairu Dada, ministan kamfanoni, kasuwanci da saka hannu jari, Niyi Adebayo, karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, da ministan harkokin sadarwa, Dakta Ibrahim Pantami.

Mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), darekta janar na hukumar NIA, Ambasada Ahmed Rufa'i Abubakar Kyari, da shugaban kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC), Mele Kolo Kyari, na cikin tawagar shugaba Buhari.

Bayan kammala taron da masu saka hannu jari a birnin Riyadh, shugaba Buhari zai zarce zuwa Makkah domin yin aikin Umrah kafin ya dawo Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel