Shugaban kungiyar ISIS, Al-Bagadadi, ya mutu

Shugaban kungiyar ISIS, Al-Bagadadi, ya mutu

A ranar Lahadi, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa shugaban kungiyar mayakan ISIS, Abubakr Baghadadi, ya mutu a wani harin da jami'an sojin Amurka suka kai masa a Arewa maso yammaci Siriya.

Trump ya bayyanawa duniya cewa sojojin sun hallaka mayakan ISIS da dama inda suka zo gab da damke Al-Bagadadi, kawai sai ya tayar da Bam ya kashe kansa.

Trump yace; "Ya tayar da rigar bam, ya kashe kansa"

"Ya mutu bayan kaiwa karshen rami na da yake buya yana kuka."

Trump ya ce an kai masa harin ne tare da gudunmuwar kasar Rasha, Syriya, Turkiyya da Iraqi.

An kwashe shekaru da dama ana neman Abubakar AlBaghadadi bayan kisan dubunnan mutanen da kungiyar yayi.

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaban kasar Rasha, Viladmir Putin ya bayyana cewa akalla mayakan kungiyar ta’addanci ta ISI guda 2,000 ne suka shiga cikin kungiyar ta’addanci ta Boko Haram domin kara musu karfi a shekarar 2018.

Shugaba Putin ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a yayin taron kasar Rasha da kasashen nahiyar Afirka dake gudana a birnin Sochi na kasar Rasha.

Biyo bayan galaba da kasashen duniya suka samu a kan ISIS a yankin gabas ta tsakiya, yawancinsu sun koma yankin yammacin Afirka domin taimaka ma Boko Haram da ta dade tana addabar Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel