Yemi Osinbajo ya nemi hakurin 'Yan Najeriya kan tashin kaya a kasuwa bayan garkame iyakoki

Yemi Osinbajo ya nemi hakurin 'Yan Najeriya kan tashin kaya a kasuwa bayan garkame iyakoki

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce an rufe kan iyakokin kasa ne saboda kasashen da ke makwabataka da Najeriya su maida hankali wajen bin dokokin shigowa kasar.

Yemi Osinbajo da yake jawabi a Garin Edo kwanan nan, ya roki mutanen Najeriya su yi hakuri da wannan mataki da gwamnatin tarayya da su ke shugabanta ta dauka na rufe duk iyakokinta na kasa.

Mataimakin shugaban Najeriyar ya yi wannan jawabi ne a wani taron ganawar da gwamnati ta yi da al’ummar jihar Edo inda ya bayyana wasu amfanin haramta shigo da kaya cikin Najeriya ta kasa.

Farfesa Osinbajo yace gwamnatin tarayya ta taimaki Manoman kasar ta. Mai girma Osinbajo ya fadi wannan ne a lokacin da wata Baiwar Allah ta koka a kan cewa farashin kayan abinci sun tashi.

KU KARANTA: An taso Ministan gona a gaba a kan batun abincin N30

A cewar sa, duk wata kasa da ta cigaba, ta na noma abin da za ta ci ne. Mataimakin shugaban kasar yake yi wa Christiana Omokaro bayani cewa bai kamata a rika shigo da abinci Najeriya ba.

“Daga cikin dalilan da su ka sa mu ka rufe kan iyakoki shi ne hana fasa-kaurin nda ake yi. Idan mu ka cigaba da bari mutanen Sin su na kawo mana kaya, za mu kashe harkar noma.” Inji sa.

“Dole sai an sha wuya domin a sha dadi. Kasashen da su ka cigaba ba su bari a kawo masu komai cikin kasarsu.” Yemi Osinbajo yace kwanan nan za a rika ganin kayan gida a kasuwannin mu.

Mataimakin shugaban kasan ya kara da cewa: “Za mu sa farashin kaya su sauko. Mu san cewa hana fasa kauri ya jawo tsada. Dole mu ba Manomanmu kwarin gwiwa domin noma ta bunkasa.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel