Tsaraba 10 da Buhari ya dawo da su daga kasar Rasha

Tsaraba 10 da Buhari ya dawo da su daga kasar Rasha

A ranar Juma'a ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dawo daga kasar Rasha inda ya halarci wani taron kasa da kasa tare da wasu gwamnoni da kuma ministocinsa.

Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya fitar da jerin abubuwan da Najeriya zata mora sakamakon ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasar Rasha.

1. Kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC) ya shiga yarjejeniya da wani babban kamfanin harkokin man fetur na kasar Rasha, LukeOil, domin cigaba da neman danyen fetur a wasu sassan Najeriya da kuma inganta matatun man fetur guda uku a Najeriya.

2. Kasar Rasha a amince da shigo wa Najeriya domin aikin gina layn dogon jirgin kasa mai tsawon kilomita 1,400 daga jihar Legas zuwa garin Calabar, jihar Kuros Riba.

3. A bangaren sarrafa makamashin iskar 'Gas', NNPC ta kara shiga yarjejeniya da babban kamfanin kasar Rasha, Gazprom, domin yin aiki tare wajen habaka sarrafa makamashin iskar 'Gas' a Najeriya.

4. Kasar Rasha ta amince da bukatar Najeriya na saka hannu wajen tashin kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta. Ana sa ran kamfanin mai girman kasa kilomita 60km zai ke samar da ton miliyan 10 na karafa daga cibiyoyi 40 da ke cikinsa. An kashe wa kamfanin karafa na Ajaokuta fiye da biliyan $8 a cikin shekaru 40.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta kama dan majalisa a APC daga arewa da hannu dumu-dumu a garkuwa da mutane

5. Rasha ta amince zata sayar wa da Najeriya wasu jiragen yaki masu saukar ungulu domin yakar 'yan ta'adda da ta'addanci.

6. Ma'aikatar tsaro ta kasa ta hada kai da gwamnatin kasar Rasha domin zamanantar da kayan aikin jami'an tsaro da kuma samar wa sojoji kayan aiki irin na sojojin kasar Rasha

7. An yi sulhu tsakani Najeriya da kamfanin kasar Rasha, ALSCON, da ke kera kayan rufi da aka yi daga sinadarin 'Aluminium'.

8. A matsayinta na kasar da ta fi kowacce kasa noman alkama a duniya, kasar Rasha ta amince zata taimaki Najeriya domin ta inganta noman alkalma.

9. Kasar Rasha ta amince zata taimaki Najeriya wajen inganta tsaro a iyakokin kasa na cikin ruwa domin maganin fashin jiragen ruwa (piracy)

10. Najeriya ta kara kulla yarjejeniya da kasar Rasha domin bunkasa bangaren hakar ma'adanan karkashin kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel