Majalisa ta aika wa tsohon gwamnan APC sammaci, ta lissafa manyan zunubansa 5

Majalisa ta aika wa tsohon gwamnan APC sammaci, ta lissafa manyan zunubansa 5

Majalisar dokokin jihar Legas ta lissafa manyan zunuban tsohon gwamnan jihar, Akinwunmi Ambode, guda biyar a daidai lokacin da ta aika masa takardar sammaci a karo na biyu.

Zunuban gwamnan sun hada da sayen wasu manyan motoci 820 ba tare da samun izini ba da kuma saba wa dokokin kashe kudi da na kaddamar da kasafin kudi a jihar.

A saboda haka ne majalisar dokokin jihar Legas ta bukaci tsohon gwamnan ya bayyana a gabanta da misalin karfe 1:00 na ranar Laraba.

Wannan shine karo na biyu da majalisar dokokin jihar Legas ta gayyaci Ambode domin ya bayyana a gabanta.

Majalisar ta fara aika wa tsohon gwamnan sammaci ne kimanin sati biyu da suka gabata, inda ta bukaci ya bayyana a gabanta tare da wasu tsofin kwamishinoninsa da hadimai.

Tuni majalisar ta kafa kwamitin da zai binciki zargin da ake yi wa tsohon gwamna Ambode na tafka badakalar kudi.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama dan majalisa a APC daga arewa da hannu dumu-dumu a garkuwa da mutane

Sai dai, a cikin wani jawabi da ta fitar, majalisar ta ce Ambode da sauran hadimansa sun ki bayyana a gabanta.

Hakan ne kuma yasa majalisar ta sake aika wa Ambode da tsofin hadimansa sabon sammaci tare da buga takardar sammacin a manyan jaridun kasar nan.

A cikin takardar sammacin, majalisar ta tuna wa Ambode muhimmanci bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi a kan manyan zunubansa guda 5 da suka lissafa.

Majalisar ta lissafa zunuban Ambode guda biyar kamar haka; 1. Dakatar da biyan wasu kudaden yi wa jihar Legas aiki ba tare da yin shawara da kowa ba 2. sayen manyan motoci 820 ba tare da izini ba 3. Ambuzzaranci da kudade na musamman da aka bawa gwamnatin jihar Legas 4. Saba wa doka wajen kaddamar da kasafin kudi da kuma 5. Kin biyayya ga dokokin gwamnatin jihar Legas a kan harkokin kudi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel