So ake yi a wulakanta ni, a bata mani suna da hukumar ICPC – Inji Okoi Obono-Obla

So ake yi a wulakanta ni, a bata mani suna da hukumar ICPC – Inji Okoi Obono-Obla

Tsohon shugaban hukumar nan ta SPIP da aka kafa musamman domin karbe kadarorin gwamnati a hannun tsofaffin ma’aikata, Okoi Obono-Obla, ya yi magana kan binciken da ake yi a kansa.

Mista Okoi Obono-Obla ya bayyana cewa cewa wasu ne su ke kokarin bata masa suna don dole. Obonpo-Obla ya yi amfani da shafinsa na Facebook, ya siffanata kansa da cikakken ‘dan kishin kasa.

A cewar tsohon Hadimin shugaban kasar, ya sadaukar da rayuwarsa a lokacin da yake bautawa Najeriya a ofishin SPIP. Kwanan nan ne dai hukumar ICPC ta yi shelar cewa ta na nemansa ido rufe.

Obono-Obla ya koka da yadda ake muzguna masa fiye da wadanda su ka saci dukiyar kasa. Obla yake cewa: “Wai meyasa wadannan mutanen k enema na? Sun karbe aikinsu, amma ba za su kyale ni ba.”

“Sun bata mani suna a gidajen jaridu, sun yi mani tarko. Sun yi mani sharri. Sun sa ana nema na. Laifin me na yi? Ko wadanda su ka saci Biliyoyin kudi ko rusa tattali ba ayi wa irin wannan wulakanci.”

KU KARANTA: Tinubu ya shiga matsalar EFCC bayan an kai korafinsa a gaban Magu

“So ake yi kurum a ci mani mutunci. Su na so ne su wulakanta ni. Su bata mani suna a idanun jama’a. Ni cikakken ‘dan kishin-kasa ne. Na yi aiki na da daraja da sadaukar da kai da jajircewa a gaskiya.”

Masanin shari’ar ya karasa kalaman na sa da cewa: “An ci mutuncin Nelson Mandela, an wulakantasa, an gurfanar da shi, aka daure shin a shekaru 27. Amma ya zama fitaccen Gwarzon Duniya.”

Obono-Obla duk ya yi wannan maganganu ne a kan shafinsa na Facebook a matsayin martani game da matakin da hukumar ICPC mai yaki da Barayi ta dauka na nemansa ruwa a jallo a Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel