Okonkwo: Ibo ya kamata su zama Shugaban kasa a 2023 domin su kadai ne ba su yi mulki daga 1999 ba

Okonkwo: Ibo ya kamata su zama Shugaban kasa a 2023 domin su kadai ne ba su yi mulki daga 1999 ba

Wani daga cikin manyan da aka kafa jam’iyyar APC da su a Najeriya, Sanata Annie Okonkwo, ya shiga cikin sahun masu neman mulki ya koma yankin Kudu maso Gabashin Najeriya a 2023.

A wata doguwar hira da Annie Okonkwo ya yi da Jaridar Vanguard, ya bayyana cewa bai kamata mulki ya cigaba da zama a Arewa bayan 2023 ba, ganin cewa yankin sun karbi mulki tun 2015.

Sanata Okonkwo yake cewa a 1999 ne Ibo su ka zo daf da samun mulki inda Marigayi Dr. Alex Ekwueme ya sha kasa hannun tsohon shugaba Olusegun Obasanjo a zaben tsaida gwanin PDP.

Okonkwo ya koka da yadda Obasanjo ya zama shugaban kasa a wancan lokaci ba tare da ya yi nasara a jiharsa da kauyensa ba. ‘Dan siyasar yace tun daga nan ne aka samu matsalar take Ibo.

KU KARANTA: An shigar da korafi kan Bola Tinubu a gaban hukumar EFCC

An zo lokacin da ya kamata manyan jam’iyyu su ba mutanen Ibo dama su yi mulki. Ba batun arziki ake yi ba, ana duba adalci ne. Wannan ya kamata jam’iyyu su yi la’akari da shi a 2023.”

Babban ‘Dan siyasar ya kara da cewa: “Bayan wa’adin Obasanjo, mulki ya koma Arewa ta hannun Marigayi Umaru Yar’Adua duk da cewa sauran mutane irinsu Peter Odili su na neman mulkin.”

“Daga baya Goodluck Jonathan ya dare kan mulki inda marasa rinjaye su ka taki sa’a. Bayan nan kuma Buhari ya zo, mulki ya sake komawa Arewa. Yanzu lokacin da Ibo za su karbi mulki ne.”

Tsohon Jigon na APC ya nemi kowa ya marawa wannan shiri baya domin a cewwarsa Yarbawa da mutanen Neja-Delta da Hausawa duk sun yi mulki, don haka yace Ibo kurum su ka rage a 2023.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel