Dubun wasu masu garkuwa da mutane ta cika a Garin Kaduna da Imo

Dubun wasu masu garkuwa da mutane ta cika a Garin Kaduna da Imo

A karshen makon nan Daily Trust ta rahoto cewa sojojin kasan Najeriya sun tabbatar da cewa Jami’ansu sun kai wani hari a inda Miyagun da su ka addabi jama’a a jihar Kaduna su ke boye.

Wani babban Jami’in yada labarai na gidan Sojan kasa, Kanal Aminu Iliyasu, ya fitar da jawabi inda ya bayyana cewa Dakarun Runduna ta 342 sun kai samame a inda wasu Miyagu su ke boye.

Aminu Iliyasu yace Dakarun na su sun farma wadanda ake zargi su na garkuwa da mutane ne a Garin Ihie a cikin karamar hukumar Ohaji/Egbema da ke jihar Imo inda aka damke mutane biyu.

Wadanda aka kama su ne Umah Kingsley da kuma wata Budurwa mai suna Chukwu Happiness. Sojoji sun same su da kananan bindigogin gida da kuma kwaban harsashin da babu komai a ciki.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga fiye da 200 sun ajiye makamai a Jihar Sokoto

Haka zalika Sojojin na Najeriya sun dura karamar hukumar Jama’a bayan an kashe wani Dattijo a Garin Janda. A nan ma Rundunar Soji ta I ta yi dacen kama wasu mutum biyu da ake zargi da laifi.

Wadanda aka kama su ne Danladi Bisallah da Manesar Danladi. Su ma dai an same su da kananan bindigogi da manyan harsashai. Wannan ya faru ne a jihar Kaduna a Arewacin Najeriya.

A wani harin kuma na dabam, an gwabza da Miyagu a Kauyukan Gindin Dutse da kuma Dajin Rijana da ke cikin kananan hukumomin Birnin gwari da Kachia duk a cikin jihar ta Kaduna.

A Dajin Rijana da Gindin Dutse, an cafke wasu Miyagu uku. An kuma samu damar karbe bindigogi uku a hannunsu. Sojojin sun kuma bayyana cewa sun ceto wani yaro da aka sace a yankin Kubau.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel