ADSIEC ta dage zaben kananan hukumomi na jihar Adamawa, ta bayar da dalili

ADSIEC ta dage zaben kananan hukumomi na jihar Adamawa, ta bayar da dalili

Hukumar Zabe na Jihar Adamawa (ADSIEC) ta dage zaben kananan hukumomi na jihar daga ranar 9 ga watan Nuwamba zuwa ranar 7 ga watan Disamba.

Shugaban ADSIEC, Isa Shettima ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikewa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a ranar Asabar a garin Yola.

Mista Shettima ya ce dage zaben ya zama dole ne saboda wasu kallubale da hukumar ta fuskanta.

Ya ce, "ADSIEC tana son ta sanar da al'umma musamman dukkan jam'iyyun siyasa da za su fafata a zaben kananan hukumomi da a baya aka shirya yi ranar 9 ga watan Nuwamba cewa yanzu an dage zuwa ranar 7 ga watan Disamba saboda matsalar zirga-zirga da wasu matsalolin."

DUBA WANNAN: Hotunan katafaren filin wasan kwallon kafa na Kahutu da Rarara ya gina

Da yake martani kan dage zaben, sakataren tsare-tsare na APC a jihar, Ahmed Lawan ya ce jam'iyyar ba tayi murna da lamarin ba amma ta dauke shi a matsayin kadara.

Mista Lawan ya ce, "Lamarin ya yi kamar jam'iyyar PDP ta razana amma za mu basu lokaci su sake shiru saboda zaben.

"Abinda kawai muke bukata kawai shine a yi wa kowa adalci a yi zabe mai tsafta."

Kazalika, shugaban kungiyar ADC, Yahaya Hammanjulde, ya ce jam'iyyar ba ta yi murna saboda dukkan 'yan jam'iyyar sun kammala shirye-shiryensu.

Mista Hammanjulde ya ce, "Ba mu yi farin ciki ba amma a matsayin mu na jam'iyya mai biyaya ga doka bamu yadda za muyi sai mu jira ranar da aka dage. Fatan mu shine a yi zabe na adalci kuma mai tsafta."

Shima a jawabinsa, Sakataren tsare-tsare na PDP a jihar, Hamza Bello ya ce jam'iyyar ta gama shirya mutanen ta saboda yakin neman zabe amma za ta dage saboda canjin.

Mista Bello ya ce, "Saboda canjin da ADSIEC suka yi ga jadawalin zaben kananan hukumomi na 2019, kwamitin zartarwa na PDP ta dage fara yakin zaben ta saboda zaben."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel