JAMB, EFCC, AMCON da sauran Ma’aikatun da su ka ciri tuta bana

JAMB, EFCC, AMCON da sauran Ma’aikatun da su ka ciri tuta bana

Ganin yadda shekarar bana ta zo karshe, jaridar Leadership ta yi wani bincike a game da ma’aikatun da su ka fi kokari a Najeriya. Daga ciki akwai irin su hukumar JAMB da EFCC.

1. JAMB

Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare na JAMB sun yi matukar kokari a bana. Bayan makudan kudin da ta tatso, JAMB ta na kan kawo muhimman tsare-tsare.

2. NCS

Wata hukuma da ta yi namijin kokari a shekarar nan ita hukumar NCS mai maganin fasa kauri. Hameed Ali ya zage dantse wajen hana shigo da kaya ta barayin hanyoyi da samun kudin shiga.

3. FIRS

Hukumar FIRS ce mai tattaro haraji a Najeriya. A karkashin Babatunde Fowler, FIRS ta yi kokarin kawo sababbin dabaru na ganin ana biyan haraji a daidai lokacin da fetur yake karyewa a Duniya.

4. FRSC

Haka zalika hukumar FRSC ta ciri tuta a 2019. FRSC ce hukumar da ke da alhakin kare jama’a a kan tituna. Hukumar ta na burin ganin an rage samun hadarurruka a kan hanyoyin Najeriya.

5. ICPC

Hukumar ICPC mai yaki da almundahana a Najeriya, ICPC da aka kirkira a 2004 ta na kan kokari na ganin ta ga bayan masu wawurar kudin gwamnati. Yanzu haka an taso wasu barayi a gaba.

KU KARANTA: PDP ta yi murnar bayan Gwamnan Ribas ya samu nasara a kotun koli

6. EFCC

Bayan ICPC, hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta na cikin hukukomin da su ke yin abin a yaba masu. EFCC ta na cigaba da bankado badakaloli iri-iri.

7. AMCON

AMCON ce ke da nauyin kula da kadarorin kasar nan. Yanzu haka hukumar ta dage wajen ganin ta karbo makukun bashin kusan Naira tiriliyan biyar da su ka makale a wasu bankunan kasar.

8. NNPC

Hukumar NNPC ta cigaba da kokarin da ta ke yi na hako danyen man fetur a Arewacin Najeriya. Kwanan nan aka hako mai a yankin Arewa maso Gabas, kuma an fara bada karfi a wasu wuraren.

9. NADDC

Kafin yanzu, Jaridar tace jama’a da-dama ba su san labarin hukumar NADDC masu kera motoci a Najeriya ba. Jelani Aliyu ya na kokari wajen ganin NADDC ta yi zarra a kasar da ma Duniya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel