2023: Matasan Igbo sun fada ma gwamnonin kudu maso gabas da su sauya sheka daga PDP zuwa APC

2023: Matasan Igbo sun fada ma gwamnonin kudu maso gabas da su sauya sheka daga PDP zuwa APC

An bukaci gwamnoni da sanatocin kudu maso gabas da su sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a matsayin wani yunkuri na tabbatar da shugabancin Igbo a 2023.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa mambobin kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo na duniya ne suka yi kiran a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba a wani jawabin hadin gwiwa dauke da sa hannun Shugaban kungiyar , Okechukwu Isiguzoro da babban sakataren ta, Okwu Nnabuike.

A cewarsu, kungiyar matasan na neman sauya shekar akalla gwamnonin kudu maso gabas biyu da wasu manyan sanatoci zuwa APC.

Kungiyar matasan tace tana neman sauya wannan al’addan na rikau da kudu maso gabas ta yiwa jam’iyyun PDP da All Progressives Grand Alliance (APGA) ta hanyar sauya sheka zuwa APC.

Matasan sun bayyana cewa ba wai kawai suna yin kiraye-kiraye bane, illa sun fara bin tsarin tabbatar da cewar an aiwatar da hakan.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin arewa basu damu da lamarin shan miyagun kwayoyi ba, inji Mallam Niga

A cewarsu, an rigada an fara tattaunawa da masu balla iko a yankin domin ganin sauya shekar ya zama gaskiya don inganta damar da kudu maso gabas ke dashi na ganin dan Igbo ya zama Shugaban kasa a 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel