Gwamnonin arewa basu damu da lamarin shan miyagun kwayoyi ba, inji Mallam Niga

Gwamnonin arewa basu damu da lamarin shan miyagun kwayoyi ba, inji Mallam Niga

Lawal Maduru, wanda aka fi sani da Malam Niga,mamallakin cibiyar horar da kangararru, ya zargin gwamnonin arewa da nuna halin ko in kula game da makomar matasa a yankin.

Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, Maduru yace gwamnonin yankin basu dauki lamarin shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa da muhimmanci ba.

Ya bayyana cewa hallayarsu na daya daga cikin abunda ke jefa yankin cikin rikici, jaridar TheCable ta ruwaito.

Maduru, wanda aka saki kan beli bayan kama shi, ya yi watsi da rahoton cewa cibiyar ya kasance zauren azaba. Ya ce manyan mutane na kawo yaransu cibiyar domin ladabtar dasu.

Yace wasu daga cikin mutanen da aka sanya wa mari anyi hakan ne domin ana su farma mutane saboda lamarinsu na tattare da shan miyagun kwayoyi da hauka.

KU KAANTA KUMA: Satar yara 9: Ganduje ya kafa kwamitin bincike game da lamarin

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta yi ikirarin rashin masaniya akan cibiyar ba saboda “ma’aikatar matasa da wasanni da sauran hukumomin gwamnati na tura masu tabin hankali cibiyar domin saita su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel